Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

Wani Mai Fafutuka A Kasar Afrika Ta Kudu Ya jaddada Muhimmacin Kafa Hadaddiyar Afrika

Dan siyasa kuma mai fafutuka a kasar Afrika ta Kudu Julius Malema ya sake jaddada kiransa na neman kafa Hadaddiyar Kasar Afrika, wadda za ta rusa shingaye na taswirar kasa da kasashen turai suka shata.

Kuma ya fadi hakan ne bayan da aka zabe shi a matsayin shugaban jam’iyyar masu fufutukar neman yancin Tattalin arziki wato EFF , kuma ita ce jam’iya ta 3 a karfi a Afrika ta kudu a zaben da aka gudanar na gama gari baya bayan nan. Ya ci gaba da cewa muna bukatar mu jagoranci Afrika, muna son mu kafa hadaddiyar Afrika mai takardar kudi na bai daya da tattalin arziki daya,da shugaban kasa daya da kuma hukumar shari’a guda daya.

Wannan dai ba shi ne karon farko da ya fara yin irin wadanan kiraye- kirayen ba. ko a watan Mayun shekarar da ta gabata ma ya fadi cewa kafa hadaddiyar Kasar Afrika barazana ce ga yan mulkin mallaka, kana ya soki shuwagabanin Afrika da suke kalubalantar burin da ake shi na kafa haddiyar Afirka.

Daga karsher ya jaddada cewa yana kan matasa ‘yan siyasa masu zuwa a nan gaba su tsaya kyam domin daga tutar kawo gyara da yakar siyasar kafa iyakokin kasashe a nahiyar Afrika da kuma fafutuka domin kafa kasar Afrika dunkulalliya da za’a kira ta da suna haddiyar Afrika.

Post a Comment

0 Comments

Close Menu