A yau Alhamis 05/11/2019 da misalin qarfe 9:24 na safe. a ka dawo katu dan cigaba da sauraron shari'ar Sheikh Zakzaky. In mai karatu bai manta ba an kwana biyu ba a waiwayi wannan shari'ar ba, tun bayan tafiyar su sheikh Zakzaky India 🇮🇳 sai yau.
Dukkan bangarorin lauyoyin da ke cikin wannan shari'a sun iso kotu. 

Banganen lauyoyin gwamnati, lauyoyin DSS, Lauyoyin 'yan sanda da kuma na su Sayyid Zakzaky duk suna cikin kotu. Sai a ka jira shigowar alkali.

Bayan Shigowar alkali kotu sai a kira case din, sai lauyan gwabnati ya miqe ya gabatar da kanshi da masu maramashi baya ya zauna. Sai lauyan su Sayyid ya miqe ya gabatar da kanshi da mai maramashi baya ya zauna.

Sai dai yau Barista Harun Magashi ne ya wakilci Femi Falana a wannan shari'a. Ya yin da Bayero Dari ke jagorantar lauyoyin gwamnati. Alkali ya shigo.

Lauyan gwamnati ya shaida wa kotu cewa an sanya ranar yau ne don ci gaba da wannan shari'a.

Daganan sai lauyan su Sayyid yafadawa kotu cewa, muna da takadda ta neman jaddada umarnin kotu don ta bayar da izinin ganawa da su Sayyid,domin tunda suka dawo daga India, Jami,an DSS basu bari angana da su ba. Kawai sai lauyan gwabnati ya fadawa kotu cewa, suna roqon kotu da ta dauke su Sayyid daga hanun DSS ta maidasu Prison,don masu son ganin su, su ringa ganinsu a cikin sauqi. 

Sai lauyoyin su Sayyid(H) sukace, munason kotu ta bar wannan baganar a yanzu, har zuwa lokacin da lauyoyin su Sayyid suka gana dasu,sai asami matsaya. Kuma da a kwai maganar da kotu tayi na cewa, aringayin case din a kusa-kusa ko kuma a ringa ware wasu kwanaki kamar uku anayin case din a jere don a gamashi da wuri, amma kotun tace, awancen lokacin su Sayyid basu yadda da hakan ba. Don haka, bata san ko haryanzu suna kan wannan ra,ayin nasu ko sun canja ba. Sai lauyoyin su Sayyid sukace, to duk wadannan abubuwan da makaman tansu, za,a iya samun mafita idan aka sami ganawa da su Sayyid din.

Daganan sai aka fara tinanin ranar da za,asanya don komawa kotun. Sai kotu tabayar da minti 15 don a kira Falana a waya, a shedamishi halin da ake ciki. Akafito daga kotu aka nemi Falana a waya ba,a sameshi ba.

Bayan da akakoma cikin kotun,sai aka shaidawa kotu cewa,ba,a sami Falana a waya ba. Amma anason ta bar komai yadda yake harsai angana da su Sayyid(H).
A qarshe dai kotun ta bayar da umarni guda biyu kamar haka:

1, Jami,an tsaro subar lauyoyin su Sayyid su gana da su duk lokacin da sukeson hakan.
2, Kuma a koma da su Sayyid(H) Prison na Kaduna.

Andage case din zuwa ranar 6 da 7 na watan Febbuary, na shekara mai zuwa. Wato 2020.