Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

Yan Adawan Guinea Za Su Kauracewa Zaben ‘Yan Majalisa


‘Yan adawa a kasar Guineea Conakry, sun sanar da anniyarsu ta kauracewa zaben ‘yan majalisar dokokin kasar na 16 ga watan Fabrairu na shekara mai shirin kamawa, sakamakon anniyar shugaban kasar na yin tarzarce a wa’adin na uku a shekara 2020.

Da yake sanar da hakan madugun ‘yan adawa na kasar, Cellou Dalein Diallo, ya ce zasu karacewa zaben saboda sabanin dake tsakaninsu da bangaren masu mulki na kasar, musamman kan batun kwakware kudin tsarin mulkin kasar.

M. Diallo, ya kara da cewa ba ma wai zasu kauracewa zaben ne ba kawai, su zura ido, zasu ma hana a gudanar da zaben.
‘yan adawan sun ce ba zasu shiga takara da shugaba Alpha Conde ba, matukar ba’a tanadi hanyoyin gudanar sahihin zabe ba.

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da zanga zangar kin jin tazarcen shugaba Alpha Conde, wanda ya sanar a makon da ya gabata shirin yin zaben raba gardama kan sabon kundin tsarin mulkin kasar.

Post a Comment

0 Comments

Close Menu