kammala karatun digiri
Laurent Simon yana da shekara hudu a lokacin da ya fara karatun firamare, amma tun kafin 'yan ajinsu su shiga babbar sakandare tuni shi yana gab da kammala digiri a shekara tara.

Shekara daya Laurent dan asalin Belgium ya dauka ya kammala matakin farko na karatun firamare ba kamar yadda sauran dalibai sukan yi ba.

Daga nan ne kwakwalwarsa ta bude cikin shekara guda ya kammala shekaru shidan da ake dauka.

Yana shekara shida ya shiga makarantar sakandare, inda ya kammala tun daga aji daya har zuwa shida cikin watanni 18.

Sai ya dauki hutun karatu kadan.

Yana da shekara takwas ya ci gaba da karatu daga gida, watanni takwas da suka wuce ya sanya kansa cikin wadanda za su kammala karatun digiri.

Karatun digiri cikin wata takwas

Laurent na son ya kirkiri sassan jikin dan adam na roba
Bayan karatun watanni takwas kacal, zai karbi shaidar kammala karatun digiri a fannin injiniya a watan Disamba.

Sai dai bai san takamaimai ta yadda ya yi karatun har ya kawo wannan mataki ba.

Lokacin da wakilinmu KD ya tambaye shi ta yaya zai samu shaidar kammala digiri yana shekara tara? Sai Laurent Simons ya kada baki ya ce, ''Ni ma ban sani ba.''

Karatun injiniya ko likita, ko duka biyun?
Laurent yana sha'awar yadda kimiyya da fasaha take taka rawa wajen samar da sassan jikin dan adam, don kundin kammala digiri da yake rubutawa yana duba ne kan wata na'ura mai alaka da kwakwalwa.

Na'urar za ta iya aunawa da kuma bibiyar abin da ke cikin kwakwalwar dan adam da gano ko akwai wata matsala.


Mahaifin Laurent ya ce ya yi farin cikin ganin dan sa a talabijin
Zuriyarsu Laurent makare take da likitoci, don haka yake sha'awar karanta bangaren likita har ya yi digirin-digirgir.

Sai dai burinsa ya wuce fannin karatu.

''Abin da nake burin yi shi ne samar da sassan jikin dan adam na roba,'' in ji Laurent mai shekara tara.

Ana amfani da sassan jikin dan adam na roba su ne wajen sanyawa wani da ya rasa wani bangare na jiki misali kafa ko hannu sandiyyar hadarin mota ko wani tsautsayi.

Ana kuma iya sanyawa koda ko zuciya hakan zai rage yawan mutuwa sanadin rashin wanda zai iya bada koda dan sanyawa marasa lafiya.

Laurent ya ce babban burinsa shi ne samar da wani abu da zai karawa mutane tsawon rai.

Dan bai wa
Manufarsa ita ce sassan dan adam na roba, sai karawa mutanen da suke bukatar wani bangaren don rayuwa da inganta lafiyarsu.


Kakannin Laurent Hans Simons da Simons s u ne na farko da suka bashi kwarin gwiwa
"Ina son ganin na taka rawa wajen karawa mutane tsawon rai, ciki har da kakannina," in ji Laurent.

A takaice dai kakanninsa ne suka gano basirarsa tun kafin ya shiga makaranta.

"Ya taso a hannun kakanninsa, sun kuma lura da baiwar da Allah ya yi masa, sai suka fara tattaunawa kan hakan.

"Mun yi tunanin kamar yadda sauran kakanni kan yi alfahari da jikokinsu, ashe sun dauki abin da muhimmanci,'' In ji Alexander Simons mahaifin Laurent.

Yanayi mai wahala
Da sannu sai malaman makarantar Laurent suka shaida wa kakanninsa baiwar da yake da ita, iyayensa suka yi kokarin gano dalilin da ya sa ya fita daban cikin tsararrakinsa?

Kwararru kansu suna mamaki da zalakarsa.


Mahaifinsa ya ce Laurenta ya na yawan magana kan shirin talabijin da aka gayyace shi
Iyayensa sun ce baya ga karatu cikin sauri, Laurent a farkon farawa yana kaunar ilimin lissafi, da kimiyya amma bai nuna sha'awa kan koyon harsuna ba.

Mahaifinsa ya ce yawancin lokuta ba ya son zuwa makaranta, sai ya yi zamansa a gida ko ya je bakin ruwa ko wasa da yara. Amma da ya fara karatun jami'a ba ya wasa, lokutan nasa baki daya na karatu ne.

"Ranar litinin take gabatar da abin da zai karanta, Talata zai shafe ta baki daya a dakin gwaji, ranar Laraba kuma karatu yake yi babu kakkautawa. Kuma a gida yake karatun na tsawon sa'a takwas.

"A ranar Alhamis yake zuwa don gana wa da shugaban tsangayar bangaren da yake karatu, ya yi tambaya kan wani abu da ya shige masa duhu, ranar Juma'a kuwa sai ya zana jarabawa,'' in ji Mahaifinsa.

Yawancin dalibai na daukar makwanni tara zuwa 12 kafin su kammala, amma shi a kwanaki biyar ya ke kammala komai.

Kuruciya
Don tabbatar da Laurenta na jin dadin karatu ba tare da matsala ba, a kan koyar da shi ba tare da sauran dalibai da ke karatun digiri ba, saboda babu tsararsa a cikinsu.


Kamar sauran yara, Laurenta na jin dadi idan ya je bakin teku
Mahaifinsa ya ce Laurent bai rasa jin dadin nan da yara sa'o'insa ke ji ba na kuruciya, saboda babu abin da ke damunsa.

Tuni ya shahara, ko shafinsa na sada zumunta na Instagram yana da mabiya 35,000, sannan yana jin dadinsa.

Ya wallafa hotunansa a bakin ruwa tare da karensa suna tattaki, yana son wasan ninkaya da son hira da 'yan jarida.

Mahaifinsa ya ce ''Yana yawan magana kan hirar da ya yi ta talabijin.''

Yaro mai tasowa

Mahaifin Laurent ya ce ya na jin dadin kuruciyarsa kamar kowanne yaro
Yaro kamar Mozart ya fara yin waka yana da shekara biyar. Picasso ya kammala zanen da ya yi na farko a lokacin da yake dan shekara tara. Amma yawanci dadin kuruciya yana yankewa yara da zarar sun fara girma.


Ko Laurenta zai banbanta da sauran yara?

"A ko da yaushe yana kokari, ya kuma ce zai iya, babu abin da zai sauya shi," in ji mahaifinsa

KNPRSCD 08
Kaduna press