Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

Yau Ne Shugaban Nigeria Zai Rattaba Hannun A Kan Kasafin kudin Shekara Ta 2020


Majiyar labaran majalisar dokokin ta Nigeria ce ta sanar da hakan, wanda ake sa ran kasafin kudin zai fara aiki daga watan Janairu zuwa Disamban shekara mai zuwa ta 2020, sabanin yadda ake fara aiki da kasafin kudina tsakiya shekara a gwamnatocin baya.

Rattaba hannun kan kasafin kudin na shekara mai zuwa ya zo ne watanni biyu bayan da shugaban Nigeria Muhammadu Buhari ya mika kasafin kudin ga majalisar dokokin kasar domin neman amincewarsu,inda cikin makwanni biyu suka kammala bincike tare da amincewa da shi.

Idan ana iya tunawa a watan Oktoban shekarar da muke ciki ne shugaba Buhari ya mika wa gammayyar majlisar dokoki ta wakilai daftarin kasafin kudin da gwamnatin ke son kashewa a shekara ta 2020 da ya kai Naira Triliyan 10.33, inda majalisar suka kara yawan kudaden da za’a kashe. kana sun kara yanayin yadda aka tsara kasafin kudin akan farashin gangar mai dala 57 mai makon dala 55 da shugaban kasar ya mika mata na gangan miliyan 2.18 na danyen man fetur da kasar ke hakowa a duk rana a hukumance.

Post a Comment

0 Comments

Close Menu