Ma’aikatar kare hakkokin bil’adama ta kasar Yemen ta yi kakkausar suka ga harin wuce gona da iri da sojojin hadakar Saudiyyar suka kai lardin Sa’ada na kasar a jiya Laraba wanda yayi sanadiyyar mutuwar wani adadi mai yawa na fararen hula a matsayin gagarumin karen tsaye ga dokokin kasa da kasa kan kare hakkokin bil’adama.

A cikin wata sanarwa da ta fitar, ma’aikatar ta ce wannan harin kari ne bisa danyen aikin da Saudiyya da kawayenta suke aikatawa a kan al’umma Yemen kana kuma lamari ne da ke nuni da yadda Saudiyya da kawayen nata suka hada kai wajen yin karen tsaye ga dokokin kasa da kasa.

Don haka ma’aikatar ta kirayi kungiyoyin kasa da kasa masu kare hakkokin bil’adama irin su Human Rights Watch, bugu da kari kan MDD da kuma kasashen duniya da su dau matakan da suka dace wajen dakatar da irin wannan wuce gona da iri na Saudiyyan da kawayenta a kan al’ummar Yemen.

Ya zuwa yanzu dai dubun dubatan al’ummar Yemen ne suka rasa rayukansu sakamakon hare-haren da Saudiyya da kawayen nata suke kai wa kasar Yemen din.