Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

Za A Bude Sabbin Madatsun Ruwa 10 A Karshen Wannan Shekarar A Iran


Minstan makamashin na Iran Rida Urdakaniyan ya bayyana cewa; Daga nan zuwa karshen wannan shekarar ta hijira shamshiyya, za a bude sabbin dam-dam har guda 10 da za su kara taimakawa wajen kara karfin makamashi a cikin kasar.

Rida Urdakaniyan wanda ya gabatar da jawabi a yau Talata a wurin bude daya daga cikin madatsun ruwa a garin Dargiz ya kara da cewa; Bude wadannan madatsun ruwan a rabin farko na shekarar bana, da kuma sauran wadanda za a bude a nan gaba, yana nuna wa duniya ne yadda muke da azama da kuma kwazo wajen samar da gagarumin sauyi a fagen ruwan sha da kuma makamashi.

Ministan ya kara da cewa; A karkashin wannan shirin za a samar da wutar lantarki mai karfin megawatt dubu uku, a cikin gundumomi 9, sai kuma filayen noma da su ka kai eka dubu 26 a cikiin kauyuka 100.

Post a Comment

0 Comments

Close Menu