Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

Za’ A Rika Gudanar Da Gasar Kwallon Kafa Ta Duniya Ta Mata Duk Bayan shekaru 2


Shugaban hukumar kwallon kafa ta duniya “FIFA” Gianni Infantino ya bayyana cewa za’a duba shawarwarin da kasar Faransa ta bayar na neman a rika gudanar da gasar kwallon kafa ta cin kofin duniya ta mata duk bayan shekaru 2, maimakon shekaru 4 da aka saba gudanarwa, saboda karbuwa da gasar ta samu daga kasashen duniya fiye da yadda ake tsammani.

Bayan da kasar Amurka ta fara karbar bakunci gasar a shekata ta 2015 ita kuma kasar Faransa ta karbi bakunci a watan Yulin da ya gabata.

Tuni dai hukumar “ FIFA” ta yanke shawarar kara yawan kulub din da za su rika halartar gasar kwallon kafa ta mata daga kulub 24 zuwa 32 a sheakra ta 2023, kuma ana sa ran a nan gaba ne hukumar za ta ayyana kasar da za ta karbi bakunci gasar a watan Yuli mai zuwa.

Tuni dai kashen Brazil, Japan, Clombiya da kuma kasar Australia suka bayyana aniyarsu na neman a ba su damar karbar bakuncin shirya gasar.

Post a Comment

0 Comments

Close Menu