Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

Za A Zabi Daya Daga Cikin “Yan Wasan Kwallo Kafa Uku A Matsayin Zakaran Afirka


Hukumar kwallon kafa ta Nahiyar Afrika CAF ta ta ce sunayen ‘yan wasan kwallon kafa guda 3 da acikinsu ake sa ran za’a zabi wanda za’a bai wa kyuatar dan kwallon Afrika na shekara ta 2019 da take gab da karewa. “Yan wasan su ne Sadio Mane dan kasar Senegal da Mohammad Salah da ya fito daga kasar masar da dukkansu suke buga wasa a club din Liverpool. Sai kuma Riyad Mahrez dan kasar Aljeria da yake buga wasa a club din Manchester city.

A ranar lahadi da ya gabata ne kwamitin kwararru na hukumar da tsoffin fitattun yan wasan kwallon kafa na Afrika suka tace sunayen guda 3. Sau biyu Mohammad Salah yana lashe kyautar yayin da shi kuma Mihrez ya lashe ta a shekara ta 2016.

Haka zalika kimanin captin da masu horar da yan wasa 54 na kungiyoyin kwallon kafa na kasashen Afrika ne za’a sanar da wadanda su ka yi nasara a cikinsu a bukin bada kyautar da za’a yi a ranar 7 ga watan janerun shekara mai zuwa ta 2020, kasar Masar .

Post a Comment

0 Comments

Close Menu