Shugaban kasar Mali Ibrahim Bubakar Kaita ya sanar da aniyarsa ta gudanar da babban taron tattaunawar kasa a wani yunkuri na kawo karshen mastalar tsaro da kasar ke fuskanta sakamakon harin da kungiyoyin yan ta’adda ke kaiwa a wasu yankuna a kasar.

Kasar mali ta fada cikin rikici ne tun a shekara ta 2012 sakamakon hare- haren kungiyoyin ‘yan ta’adda masu ikirarin jihadi da hakan ya jawo rashin tsaro a wasu sasssan kasar.

Har ila yau ya kara da cewa yana farin ciki sosai game da wannan shiri da aka bullo da shi inda bangarori daban- daban na kasar za su yi musayar ra’ayi domin samar da mafita game da irin mataken da ya kamata a dauka wajen kawo karshen matsalar tsaro da ya dabaibaye kasar.

A nata bangaren shugabar mata a kasar ta Mali Korotum Bello ta bayyana cewa tattaunar kasar za ta bayar da dama ga mahukuntan kasar wajen samar da mafita game da matsalar tsaro da ta dade yana ciwa kasar tuwo akwarya.