Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

Za'a Gudanar Da Zaben Raba Gardama A Sudan Ta Kudu


Gwamnatin kasar Sudan ta kudu ta sanar da cewa mafita na fita daga rikicin siyasa da kasar ke fama da shi, a gudanar da zaben raba gardama a yankunan da suka ki amincewa da yarjejeniyar sulhu.

Jaridar Sudan tarbiyun mallakin kasar Sudan ta habarta cewa a jiya lahadi gwamnatin kasar Sudan ta sanar da cewa shugaban kasar Salva Keir na ganin cewa gudanar da zaben raba gardama a yankunan da suka ki amincewa da yarjejeniyar sulhu ita ce hanya daya cilo na kawo karshen rikicin cikin gida da kasar ke fama da shi.

Shugaba Keir ya kara da cewa zaben raba gardama shi zai iya warware rikicin siyasa da kuma tabbatar da tsaro musaman ma a yankunan da suke adawa da shirin gwamnati na tabbatar da sulhu a tsakanin al'ummar kasar.

A ranar larabar da ta gabata ce shugaban keir ya gana da wakilai 32 na yankunan kasar da kuma jam'iyun siyasa da nufin amincewa da shirin gwamnati na sulhu, to saidai taron ya tashi ba tare da cimma matsaya ba.

Post a Comment

0 Comments

Close Menu