Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

Za’a Rantsar Da Sabon Shugaban Kasar Aljeria A Makon Gobe


Gidan talbijin din kasar Aljeria ba tare da bayyana takamaiman lokaci ba ya sanar da cewa za’a gudanar da bukin rantsar da Abdulmajid Taboone a matsayin sabon shugaban kasar a makon gobe bayan da ya lashe zaben shugaban kasa da aka gudanar da ke cike da rudani, ina da ya samu kashi 58 % na kuri’un da aka kada, bayan da jama’a da dama suka kaurace wa rumfunan zabe.

Bisa ayar doka ta 89 ta kundin tsarin mulkin kasar za’a rantsar da zababben shugaban kasa a gaban majalisar mako guda bayan sanar da sakamakon zabe, kuma zai kama aiki a nan ta ke.

A yau ne ake sa ran hukumar zabe ta kasar za ta mika rahoton karshe game da zaben shugaban kasa da aka gudanar ga majalisar dokokin kasar , yayin da ita kuma a cikin wannan makon nan za ta sanar da sakamakon zabe na karshe duk da yake cewa babu wani dan takara da ya nuna rashin amincewa da sakamakon zaben .

Post a Comment

0 Comments

Close Menu