Gwamnatin kasar Zambiya ta bukaci jakadan kasar Amurka ya fice daga cikin kasar saboda katsa landan din da yake yi a cikin al'amuran cikin gidan kasar
Kamfanin dillancin labaran Fars ya nakalto Edgar Lungu shugaban kasar Zambiya a jiya lahadi na cewa mun bukaci jakadan kasar Amurka Daniel Foote da ya gaggauta ficewa daga cikin kasar.

Shugaba Edgar Lungu ya ce ya
dauki wannan mataki ne sakamakon katsa landar din da jakadan kasar Amurka ke yi a harakokin cikin gida na kasar musaman ma kan yadda yadda Mista Foot jakadan na Amurka ya yi kakkausar suka kan hukuncin shekaru 15 da wata kotu da yankewa masu auren jinsi daya a kasar.

Har ila yau Shugaban kasar ta Zambiya ya ce sun aike da korafinsu kan hukumomin birnin Watsington, kuma suna jiran amsar da za su bayar.