Gwamnatin Amurka ta sanar da dakatar da dukkanin ayyukan ofisin jakadancinta a birnin Bagadaza na Iraki.

tashar Almanar ta bayar da rahoton cewa, a jiya Ofishin jakadancin Amurka ya sanar da dakatar da dukkanin ayyukan ofishin kasar da ke birnin Bagadaza, inda ake sa ran dauke wasu ayyukan zuwa wani yanki.

Rahoton ya kara da cewa, Amurka ta dauki wannan matakin ne bayan da al’ummar kasar ta Iraki suka kone ofishin jakadancin an Amurka da ke birnin Bagadaza, inda jakadan na Amurka ya sha da kyar, sakamakon harin da Amurkan ta kai a kan dakarun sa kai na al’ummar Iraki.

Ofishin jakadancin an Amurka ya ce zai mayar da wasu daga cikin ayyukans zuwa birnin Arbil.