Al'ummar yankin zirin Gaza a Palestine sun kona tutocin Amurka da Isra'ila a juyayin kisan Kasim Sulaimani.

Tashar Almayadeen ta bayar da rahoton cewa, a jiya Al'ummar yankin zirin Gaza a Palestine sun kona tutocin Amurka da Isra'ila a juyayin kisan Kasim Sulaimani.
Rahoton ya ci gaba da cewa, daruruwan jama'a ne a cikin fushi suka gudanar da angami a garin Gaza, inda suke la'antar Amurka da Isra'ila da kisan da suka yi wa janar Kasim Sulaimani.

Masu gangamin sun rika rera taken cewa, dukkanmu Sulaimani ne, kuma daukar fansa kan kisan sa ya zama wajibi, tare da bayyana cewa al'ummar falastinu tana tare da shia  tafarkinsa na gwagwarmaya da manyan azzalumai na duniya.

An gudanar da irin wanann gangamia  jiya juma'a  da kuma ya a Asabar kasashe daban-daban, domin yin tir da kisan Kasim Sulaimani, wanda masana ke ganin shi ne ya karya lagon 'yan ta'adda da ke samun goyon bayan Amurka a siriya da kuma Iraki, lamarin da bai yi wa Amurka da 'yan korenta da e yankin dadi ba.