Wata mata musulma ta bayyana cewa an kore ta daga aiki a Fast Foody da ke Dalas a Amurka saboda lullubi.

Wata mata musulma mai suna Folake Adebola, ta bayyana a shafinta na twitter cewa shugabanta ya kore ta daga aiki saboda lullubi da take sakawa a knata.
Wannan lamari ya faru ne a dakin cin abinci na Chicken Exress da ke yankin Port Worth a garin Dalas na jihar Texas da ke kasar Amurka.

Matar ta saka hoton bidiyo na lokacin da take bayyana wa shugaban nata cewa, tana saka lullubi ne saboda addininta na musulunci, amma shi kuma yana cewa hakan ya saba wa ka’idar aikinsa.

Ta bayyana cewa ta karbi addinin musulunci ne daga bisani, kuma yarda cewa saka lullubi ga mata a cikin addinin muslunci wajibi ne, akan haka take sakawa.

Ta kara da cewa a wan shekare ta zo aiki sai aka sanar da ita cewa an kore ta, saboda taki ta daina saka lullubi a kanta, ta bayyana cewa wannan wariya ce da banbanci aka nuna mata saboda addininta.