Da'irar Kaduna karkashin jagorancin wakilin 'yan 'uwa na Kaduna Malam Aliyu Umar Tirmizi na ci gaba da gabatar da wani karatu

musamman wanda Hujjatul Islam Wal Muslimeen Shaikh Shu'aibu Muhammad Qum ke gabatarwa ga wakilai da wasu ba'adin 'yan uwa almajiran Sayyid Ibraheem Zakzaky (H) masu bukata.

Ana dai ci gaba da gabatar da karatun, wanda muka samu tsarabar wasu hotunan zaman karatun na yau Asabar 25/1/2020.

Ga duk mai sha'awar shiga karatun, yana iya tuntubar inda ya san yana samun sakon da'ira don jin lokaci da kuma wurin da ake gabatar da karatun kafin a rufe.

Ga wasu hotunan yadda karatun ke gudana: 
Kaduna press
KNPRSCD 08