shafin islamicnews.org.sa ya habarta cewa, masu yaki da akidar nuna kyama ga musulunci na cibiyar Azhar sun fitar da bayani da ke tir da matakan da masu kiyayya da muslunci a Holland suke dauka.
Bayanin ya ce irin wadannan matakai babu abin da suke jawowa in banda fitina a tsakanin al’ummomi, domin kuwa hakan yana a matsayin tsokana ne ga dukkanin musulmi na duniya baki daya.

Haka nan kuma sun bukaci mahukunta a kasar Holland su dauki matakan da suka dace domin taka burki ga masu yunkurin fitar da zane-zanen batunci ga manzon rahma a kasar.

Kamar yadda bayanin ya ce sau tari a kan samu masu satsauran ra’ayi daga dukkanin bangarori na mabiya addinai, wanda uma wasu lokuta ayyukan tsokana kan iya jawo fitina a tsakaninsu, wanda zai iya shafar wadanda ba su ba su gani ba.

Dan majalisar dokokin kasar Holland mai tsananin kiyayya da addinin muslunc, ya shirya gudanar da wata gasa ta zane-zanen batunci a kan manzon Allah (SAW) wadda za a gudanar nan ba da jimawa, lamarin da ke ci gaba da jawo cece ku ce a duniya.

Ko a shekarun baya ma ya taba yin wani makamancin hakan, inda ya rubuta wani littafi mai suna fitina, inda ya wulakanta kur’ani mai tsarki da kuma yin izgilin ga addinin musulunci