Rahotanni daga kasar Libya na cewa, mayakan da suke yin biyayya ga Khalifa Haftar sun kaddamar da hare-hare da rokoki a kan wasu unguwannin birnin Tripoli fadar mulkin kasar ta Libya.

Kamfanin dillancin labaran Anadolu ya bayar da rahoton cewa, a jiya ne majalisar yankin Benghazi ta sanar da cewa, yarjejeniyar dakatar da bude wuta ta kawo karshe, inda bayan ‘yan sa’oi da bayar da wanann sanarwa, dakarun haftar suka fara ruwan wuta kan birnin Tripoli.

Rahotanni sun ce hare-haren sun fi tsananta a kan yankunan Ramlah da kuma Salahuddin da ke kudancin birnin Tripoli.
Wannan labarin na zuwa ne bayan taron da aka gudanar na birnin Moscow, inda kasashen Rasha da Turkiya suka jagorancin zaman sulhunta bangarorin da ba sa ga maciji da juna na kasar ta Libya, taron da bai cimma burin da ake bukata ba.

Haftar ya bayyana cewa yaki sanya hannu kan yarjejeniyar dakatar da bude wuta a Moscow ne, saboda halartar Turkiya a wurin, wadda ya zarga da taimakawa ayyukan ta’addanci a kasar Libya