Hukumar zabe mai zaman kanta a Guinea Bissau ta sanar da dan takaran adawa Umaru Sissoko Emballo, a matsayin wanda ya lashe zaben shugabancin kasar zagaye na biyu.

Dan takaran adawa wanda shi ma tsohon firaministan kasar ne, ya lashe zaben ne da kasha 53,55% na yawan kuri’un da aka kada, a yayin da babban abokin hammayarsa tsohon firaministan kasar Domingos Simoes Pereira, ya samu kasha 46,45%, kamar yadda shugaban hukumar zaben kasar José Pedro Sambu, ya sanar yau Laraba.

Mista Sissoko, dan shekaru 47, ya taba rike mukamin firaministan kasar a karkashin gwamnatin shugaban kasar mai barin gado, José Mario Vaz, a tsakanin shekara 2016 zuwa 2018, kafin daga bisani ya fice daga cikin jam’iyyar (PAIGC), mai mulki ya kafa ta shi jam’iyya (Madem).

Nasarar, Umaro Sissoco Embalo, ta rufe babin jam’iyyar ta (PAIGC), wacce ta zo ta farko a zaben shugabancin kasar zagayen farko.

Kasar Giunea Bissau, wacce ta samu yancin kanta a shekara 1974, daga turawan mulkin mallaka na Portigal, ta jima tana fuskantar juyin mulki, wanda daga lokacin zuwa yanzu ya fuskanci juyin mulki hudu da kuma yunkurin juyin mulki 16.