Minista mai kula da shimfida hanyoyi na Iran ya bayyana haka yana mai kara da cewa; Ma’aunin tattalin arzikin Iran yana tafiya daidai, domin a halin yanzu kayan da Iran take fitarwa waje ya fi wanda ta ke shigo da su yawa.

Muhammad Salami wanda ya kaddamar da wasu sabbin aikace-aikace na gwamnari a gundumar Ardebil a jiya Laraba ya kara da cewa; A karkashin takunkumi na zalunci da Amurka ta kakaba wa Iran, kasar tana zama wani babban kamfani da ake ci gaba da kere-kere a muhimman bangarori da su ka hada, na gine-gine, ruwa, wutar lantarki da kuma iskar gas.

Dangane da gidajen da gwamnati ta ke ginawa da sayar da su ga talakawa cikin rahusa, ministan ya ce; gwamnati za ta ci gaba da kokari domin kawo karshen duk wasu matsaloli da ake fuskanta a wannan fagen.