A Jiya Juma’a ne aka kawo karshen gasar kokawar shekara - shekara domin lashe kofin Takhti na kasa da kasa, a garin Shiraz.

“Yan kokawa 116 da su ka fito daga Iran da wasu kasashe daban-daban ne su ka shiga cikin gasar.

Iran ta zo ta daya,sai kasar Armenia ta biyu da kuma Tajikistan ta uku.

A kokawar karshe ta masu ajin kilogram 55, Pouya Nasser ne ya sami galaba akan Pouya Dadmarzm, da hakan ya sa shi samun kyautar zinariya.

Sai kuma Meysam Delkhani daga ajin masu nauyin kilogram 63, da kuma Muhammadi Assadi da sukkaninsu su ka sami kyautar zinariya.

Ana yin wannan kokawar ta gargajiya ne domin tunawa da fitaccen dan kokawar Iran Golamreza Takhti ( 1930-1968) wanda ya sami kyautuka masu yawa na zinariya da tagulla a wasannin Olympics daban-daban.