A jiya ne da misalign karfe 8 na safe  Ayatollah Sayyid Ali Khamenei ya jagoranci sallar janaza a kan gawar Shaheed Qassem Sulaimani da kuma sauran wadanda suka yi shahada tare da shi.

Kafin fara sallar dai diyar Qassem Sulaimani mai suna Zainab ta gabatar da bayania  wurin, inda ta bayyana cewa; mahaifinta tare da sauran shahidan sun rasa rayukansu ne wajen kare kare martabar al’umma, kuma taron miliyoyin mutane a Iraki da Irana  okacin raka gawawwakinsu sako ne a fili ga Amurka.

Shi ma a nasa bangaren shugaban kungiyar Hamas Isma’ila Haniyya ya gabatar da nasa jawabin da aka saka kai tsaye da Gaza, inda ya jinjina wa Shahid Sulaimani, tare da bayyana shi a matsayin babban ‘yan gwagwarmaya da ‘yan mulkin mallaka na wannan lokaci.

Miliyoyin mutane ne dai suka taru a birnin na Tehran, inda aka dauki tsawon sa’oi kafin isar da gawawwakin zuwa dandalin ‘yanci da ke Tehran, saboda cunkoso na miliyoyin jama’a.