Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

Jagora:Yerjejeniyar Karni Ba Zata Kai Labari Ba


Jagoran juyin juya halin musulunci Ayatullahi Sayyeed Aliyul Khaminae ya bayyana cewa yerjejeniyar karni wacce shugaban kasar Amurka Donal Trump ya gabatar a shekaran jiya, da yardan Allah ba za ta kai labari ba.

Jagoran ya bayyana haka ne a shafin ofishinsa na Tweeter, ya kuma kara da cewa al-ummar musulmi ba za ta taba manta da al-amarin Palasdinawa ba.

Dangane da shirin yahudantar da birnin Qudus kuma, jagoran ya ce maganar banza ce gwamnatin Amurka da yahudawan suke fada, don maida birnin Qudus ya zama cibiyar gwamnatin HKI ba abin amincewa bane ga dukkan musulmi na kirki.

A ranar tarlatan da ta gabata ce shugaban kasar Amurka Donal Trump ya gabatar da shirinsa na zaman lafiya a gabas ta tsakiya wanda ya kira shi “Yerjejeniyar karani”, sannan a fadin fadar white House wannan ita ce yerjejniye mafi inganci wacce aka taba gabatarwa dangane da wannan matsalar.

Yerjejeniyar dai ta biyawa yahudawan Isra’ila duk abinda take so dangane da kafuwar HKI kan kasar Palasdina.

Post a Comment

0 Comments

Close Menu