Jakadan kasar Burtaniya a Tehran Robert Macaire ya fice daga kasar Iran kwanaki kadan bayan tsare shi da jami’an tsaron kasar Iran suka yia.

Tashar talabijin ta Presstv ta bayyana cewa jakadan ya bi tsarin diblomasiyya ta ficewa daga kasar a wannan ficewarsa.

Kafin hakadai jami’an tsaron kasar sun kama jakada Macaire na mintuna 15 kafin ya bayyana cewa shi jakadan kasar Britaniya ne. Da haka kuma jami’an tsaron suka sallame shi bayan samun tabbaci daga ma’aikatar harkokin wajen kasar.

An kama jkadan ne a wani wurin da wasu mutane a birnin Tehran suke gudanar da zanga-zangar da bada da izini yana tunzura masu zanga-zamgar da kuma daukar hotuna.

Jami’an gwamnatin Iran da dama sun nuna fushinsu da yadda jakadan ya halarci zanga-zangar masu adawa da gwamnatin kasar.

Masu zanga-zangar dai wai suna nuna fushinsu ne da kakkabo jirgin fasinjar kasar Yukrai wanda da kuskure dakarun juyin juya halin kasar suka cilla masa makami mai linzami wanda kuma ya yi sanadiyyar faduwarsa da kuma kissan mutane 176 mafi yawansu iraniyawa