Babban kwamandan hafsoshin soji na Iran ya bayyana cewa, barazanar kai hari kan wurare 52 a Iran za ta bayyana ga kowa a ina ne wadannan alkalumman na 5 da 2 suke.

kwamandan Hafsoshin sojojin kasar Iran Manjo Janar Abdurrahim Mousavi ya yi watsi da barazanar da shugaban Amurka Donald Trump ya yi na kai hari kan muhimman wurare 52 na kasar Iran, kuma ya bayyana cewa Amurka ba ta da karfin gwiwar da za ta iya aiwatar da alkwarin kura da ta dauka.

Kuma wannan ya zo ne kwana daya bayan da Trumph yayi barazanar kai hari kan muhumman wurare guda 52 na Iran da suka hada da wurare na ala’adu matukar Iran ta mayar da martani game da hari da jirgin Amruka mara matuki ya kai kan babban kwamandan yaki na kasar iran Janaral Qasim Sulaimani a daren juma’a a kusa da filin jirgin sama na birnin Bagadaza da hakan ya yi sanadiyar shahadarsa da wasu mukarrabansa.

Ya ci gaba da cewa Trumph ya yi wadannan kalaman ne domin rufe danyen aiki da tafka na kashe janar Qasim Sulaimani.
A nasa bangaren ministan harkokin wajen kasar Iran Jawad Zarif a wani sako da ya aike da shi a shafinsa na Twitter ya bayyana cewa kai hari kan muhimman wurare da suka shafi aladu tafka laifin yaki ne, kuma zai kawo karshen zaman Amurka a yankin yammacin Asia baki daya.