A jiya Laraba ce majalisar dokokin tarayyar Turai a birninBrussels Brussies ta amince da ficewa kasar Birtaniya daga kungiyar tare da rinjaye mai yawa, inda ‘yan majalisa 621 suka amince sai kuma 49 suka ki amincewa.

Tun bayan zaben raba gardama da aka gudanar a ranar 23 ga watan Yunin shekara 2016 ne Birtaniya take gwagwarmayan fita daga kungiyar ta EU, amma sai a makon da ya gabata ne majalisar dokokin kasar ta amince da dokar ficewar, sanna sarauniyar Ingila kuma ta sanyawa dokar hannu.

Don haka daga gobe jumma’a 31 ga watan Jenerun shekara ta 2020 kasar Birtaniya za ta fice daga tarayyar Turai, sai dai za ta ci gaba da zama mamba a hadaddiyar kasuwar Turai, sannan zuwa karshen shekaran nan da muke ciki, za’a yi ta kulla sabbin yerjeniyoyi tsakaninta da sauran kasashen na Turai da kuma kasashen duniya.