Majalisar dokokin kasar Masar, ta amince da tsawaita doka ta baci dake akwai a kasar da watanni 3, saboda kalubalen tsaro da kasar ke fuskanta.

Wani mamban a majalisar dokokin kasar, Mohammed Abou-Hamid, ya shaidawa kamfanin dilancin labaren Sin na (Xinhua) cewa, majalisar ta amince da dokar shugaban kasar ta tsawaita dokar ta baci a kasar da karin wasu watanni 3, daga ranar 27 ga watan Junairun da mu ke ciki.
Karkashin dokar dai, sojoji da 'yan sanda za su dauki dukkan matakan da suka kamata, wajen tunkarar ta'addanci da tabbatar da tsaro a duk fadin kasar.

An sanya doka ta baci a kasar ne a karon farko, a watan Afrilun 2017, bayan hare-hare da aka kai wa wasu mujami'u 2, wadanda suka yi sanadiyar mutuwar mutane 47, Kuma tun daga wancan lokacin ne ake ci gaba da tsawaitata.

Abou-Hamid ya ce, tsawaita dokar za ta ba wa hukumomi masu ruwa da tsaki a tabbatar da tsaro a cikin kasa, amfani da damar da doka ta ba su na yaki da ta'addanci, yana mai cewa, daukacin ‘yan dokokin kasar ne suka kada kuri'ar amincewa da tsawaita dokar.