Majiyar Rundunar tabbatar da zaman lafiya ta kasa da kasa a yankin Darfur ( UNAMID ) ta bayyana cewa ya zuwa yanzu mutane 24 ne aka tabbatar da mutuwarsu sakamakon wani hari da aka kai a sansanin yan gudun hijira na Krinding da ke lardin Darfur da yaki ya daidaita.

Majiyar ta ci gaba da bayyana cewa wani rikici ne ya barke tsakanin larabawa da sauran kabilun Afrika, inda larabawan suka kai hari kan sasasanin yan gudun hijran kuma an ji karan harbe- harbe da kuma cinna wuta a sansanin da ya kai ga kashe mutane da dama da kuma jikkata wani adadin mai yawa.

Sai dai iyalan wadanda abin ya shafa sun garzaya asibiti inda suka yi barazanar kashe ma’aikatan asibitin tare da lalata wurin ajiyar Jini, kuma sun kashe wani dan sandan gwamnati a lokacin da yake kokarin shiga tsakani.

Samar da dawammar zaman lafiya a yankin Darfur da sauran yankun kasar suna daga cikin babban kalubale dake fuskantar gwamnatin gambizar kasar tun bayan kifar da gwamnatin tsohon shugaban kasar Umar Al’bashir a watan Aprilun da ya gabata.

Rikicin yankin Darfur ya barke a shekara ta 2003 bayan da kabilun da ba larabawa ba suka shelanta yaki kan gwamnatin Khartum da ya kai ga kashe mutane sama da 300,000 tare da tilastawa miliyna 2.5 barinn gidajensu , da kuma sama da miliyan 180,000 tarwatsewa a yankin Darfur.