MUZAHARAR NEMAN A SAKI SHEIKH ZAKZAKIY A DA'IRAR KADUNA
-KADUNA PRESS.

A yau asabar 11/01/2020 ma 'yan uwa musulmi sun sake fitowa domin kara jaddada kiransu ga hukumomin Nigeria akan su gaggauta sakin Jagora Sheikh Zakzakiy da mai dakinsa Malama Zeenat, daga tsarewar haramcin da hukumomi ke yi musu tun a karshen shekara ta 2015.

Tsarewar tasu dai ta biyo bayan farmakin da jami'an sojojin Nigeria suka kai masa a muhallinsa dake cikin unguwar gyallesu a cikin garin Zarian jihar kadunan Nigeria, bayan da suka kashe mabiyansa fiye da dubu 1000+, suka jikkata da dama daga cikinsu kana suka kame daruruwa daga ciki.

Muzaharar wadda 'yan uwan suka gudanar sun farata ne daga gombe road by ahmadu bello way tudun wada kaduna, da misalin karfe 06:00pm na yamma, Kuma suka rufeta a layin bayajidda street by kano road.

Sun dai fara kuma sun kammala lami-lafiya, Kamar yadda suka saba, ba tare da wani tayarwa da al'umma hankali ba.
-J.S.A
-KNPRSCD 06.
-11012020.