MUZAHARAR NEMAN A SAKI ZAKZAKIY A DA'IRAR KADUNA!!!
-KADUNA PRESS.

A yau talata 21/01/2020 ma 'yan uwa musulmi almajiran Sheikh Zakzakiy sun sake fitowa domin kara jaddada kiransu ga hukumomin gwamnatin Nigeria akan su gaggauta sakko Jagora Sheikh Zakzakiy da mai dakinsa Malama Zenatuddeen Zakzakiy.

Sheikh Zakzakiy dai yana tsarane tun shekaru kusan hudu da suka gabata, bayan farmakin da jami'an tsaron kasar Nigeria suka kai masa a mazauninsa dake gyallesu cikin birnin Zaria.
'Yan uwan sun fito mazansu da matansu, manyansu da yara,

Muzaharar dai ta gudana ne akan titin poly to k/bacci a birnin garin na kaduna, inda suka faro muzaharar daga poly gate, suka dauki hanyar kasuwan bacci suka rufe ta a k/bacci round about. Kaduna.

An dai fara kuma an kammala lami-lafiya saboda rashin halartar jami'an tsaro muzaharar.
-KNPRSCD 06.
-J.S.A
-21/01/2020.