-KADUNA PRESS.

A yau litinin 06/01/2020, 'Yan uwa musulmi almajiran Sheikh Zakzakiy na Da'irar Kaduna da kewaye sun gudanar da muzaharar Allah wadai da kisan gillar da jami'an sojojin Amurka suka yiwa shugaban askarawan kare daular musulumci ta Iran General Qasim Sulaemaniy da Abul Mahdiy almuhandis a hanyarsu ta zuwa birnin bagadaza dake Iraqi.

Suleimani dai General ne da akayi ittifakin ba'a taba yin kamarsa ba daga 1980's zuwa yanzu, ta yadda ya zamarwa abokan gabar kasar ta Iran wani karfen-kafa wanda babu yanda zasuyi dashi, shine ma yasa wasu ke ganin cewa dalilin da yasa sukayi duk yanda suke ganin zasu iya yi wajen ganin sun halakashi.

'Yan Uwan dai sun fito ne mazansu da mata manya da yara domin nuna alhininsu akan wannan kisa da Amurka tayiwa wadannan bayin Allah mutum biyu, da Kara jaddada kiransu ga gwamnatin Nigeria akan ta gaggauta sakin Jagora Sheikh Zakzakiy daga haramtacciyar tsarewar da take masa bisa zalinci, bayan farmakin da jami'an sojin Nigeria suka Kai masa a karshen shekarar 2015 a muhallin sa dake gyallesu, bayan kashe mabiyansa sama da mutum dubu 1000+ da kame daruruwa daga ciki, sannan suka kameshi suka tafi dashi.

Muzaharar dai sun fara tane karfe 06:00pm, daga kan layin Ibrahim Taiwo road by Ahmadu Bello way dake tsakiyar birnin Kaduna,
Masu muzaharar suna tafe suna rera baitocin MUTUWA GA AMURKA, MUTUWA GA ISRA'ILA, GWAMNATI KI SAKI SHEIKH ZAKZAKIY, a harshe turanci (DEATH TO AMERICA, DEATH TO ISRAEL, GOVERNMENT FREE SHEIKH ZAKZAKIY), muzaharar tabi kan titin Ahmadu Bello way ne, inda aka rufe muzaharar a liventis round about.

Bayan kammala muzaharar ne 'yan uwan suka gabatar da Rally duk domin gabatar da Allah wadai dinsu akan kasar Amurka bisa kisan G. Suleimani da Almuhandis, inda suka zagaye round about din suna Kara jadda DEATH TO AMERICA DEATH TO ISRAEL, 'Yan uwan sun dauki mintoci a kewaye da round din kafin daga bisani akayi kabbarbari aka sallami kowa da kowa.
-J.S.A
-KNPRSCD 06.
-KADUNA PRESS.
-06012020.