MUZAHARAR NEMAN A SAKI SHEIKH ZAKZAKIY A DA'IRAR KADUNA...
-KADUNA PRESS.

A yau juma'a 31/01/2020 'yan uwa musulmi almajiran Sheikh Zakzakiy sun sake fitowa domin kara Jan kunnen gwamnatin da suka kira da ta kama-karya ko kama-kashe data gaggauta sakin Jagora Sheikh Zakzakiy ba bisa ka'ida ba, kamar yadda babbar kotu ta shida mai mazauni a Abuja wadda Mr. Kolawale ke jagoranta tayi umarni a kusan shekaru uku da suka gabata.

Muzaharar wadda Shaikh Aliyu Tirmidhiy ya jagoranta anfarata ne karfe uku 03:00pm na rana, kuma anfarota ne daga kan layin Kano road aka bi hanyar Ahmadu Bello way aka nufi levintis round about, aka nufi hanyar bakin dogo aka rufe muzaharar a junction din 'yan tumatir.

Andai fara kuma ankammala muzaharar lami-lafiya.
-KNPRSCD 06.
-J.S.A
-31/01/2020.