‘Yan wasan Najeriya suna taka rawar gani a wasannin neman cancantar zuwa gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya da za a gudanara shekara ta 2022.

A zantawarsa da mane labarai, Voictor Ikpeba tsohon dan wasan Najeriya ya bayyana cewa, ya yaba da yadda yaga wasan super eagles a baya-bayan nan.

Ya ce ya samu karfin gwiwa matuka dangane da wasan na super eagles duk kuwa da kunnen dokin da suka yi a ranar Talata, amma duk da haka su ne sukeda karfi a rukunin C, wanda ya hada su Afrika ta tsakiya, Cape Verde da kuma Liberia.

Victor Ikpeba ya kara da cewa, yana da imanin cewa bayan wasannin cin kofin kwallon kafa na duniya na shekara ta 2022, matsayin da Najeriya take da shi ta fuskar kwallon kafa zai sama.

Tsohon dan wasan na Najeriya dai ya kasance daga wadanda suka buga wa kasar wasannin cin kofon kwallon kafa na duniya a shekarun 1994 da 1998, kuma yasaka wa Najeriya kwalle, kamar yadda kuma tauraronsa ya haska a kasashen turai a lokacin da yake buga kwallon kafa.