*SAQUN TA'AZIYA DA TAQAITATCEN TARIHIN MARIGAYI ARAMMA MALAM JAMIL MUSA*

Muhammad Suleiman Abdullah ✍

Haqiqa munyi babban rashi a garin KadunaYau da rana misalin qarfe 03:43pm nasamu labarin da girgiza zuciyata na rasuwan Aramma Malam jamil musa.

Shidai Malam jamil babban bawan Allah ne, ma abocin gudun duniya da neman lahira.Duk Wanda yasanshi to yasanshine a hanya biyu ko neman ilimi ko bada ilimi tabbas anrasashine a lokacin da ake tsananin buqatarshi.

Duk dacewa ni yarone qarami kuma nasan Malam jamil ne a lokaci kadan narayuwata Wanda be wuce shekara biyu ba zuwa biyu da rabi ba, Amma nasamu abubu da yawa a tartare dashi, kuma nakuya dabarun neman ilimi dayawa a gurinsa.

Malam jamil yakasance malami a jami'atul mustapa ta duniya Wanda reshenta ke garin Kaduna.

Kuma yataso a gidan ilimine domin baban shi babban malamine a Tudu/wata cikin garin Kaduna domin kuda mahaifinsa yarasu Sayyeed Zakzaky (H) ne yaja goranta yimasa sallahr jana'iza

Malam jamil mahaddacin al-qur'ani ne kuma baru bucin al-qur'ani ne domin ya rumuta Qur'ani da hannunsa, kuma yabada Qur'ani ga Jagoranmu Sayyeed Zakzaky (H) kuma Sayyeed (H) yakai wannan Qur'ani a haramin imamu aliyu ar-rida (AS) dakansa.

Haqiqa Malam jamil yasan Jagora Sayyeed Zakzaky (H) fiye da fadina domin ni agunsa naqara fahimtar jagora (H) kuma kuda yaushe qarfafata yakefi akan neman 'yancin jagora (H) yakance min inasamu hali inkoma abuja kuma mudage da fita a garin Kaduna.

Malam jamil Yakasance shine babban malami a duk lokacin da ake karatun daura a fadin qasar nan kuma kuwana dalibi yana maraba da karatunsa domin yagoge a 6angaran kuyarwa.

Malam jamil yakafa makaran zaure a gidansa  wace ake karatu da a suba kuma wannan karatu ya matuqar temaka wa matasanmu domi musha ilimi namusanman a gurinsa.

Duk da wannan matsayin nasa bai daukansa waniba yakuma qaramar makaranta ta iftida'iya yana bada gudun wama ga yara qanana, domin yacigaba da kuyarwa a fudiyyah rigasa, Kuma yacigaba da kuyarwa a Iqamatu Dinul Islam Rigasa kuma suce yakawu wa makarantar cigaba mai tarin yawa.

Yakasance yakanyi jawabi a munasabubi in anboqaci da yayi jawabin.

Ni naji da kunnena yana cuwa lazimne 02:00 am (na dare) nayi sai yafarka kunga irin wadanna bayin Allah.

Ina miqa ta'aziya ga iyalinsa ya 'ya'yansa.

Ina miqa ta'aziya ga da'irar kaduna bakidaya.

Ina miqa ta'aziya ga 'yan uwana dalibai.

Ina miqa ta'aziya ga duk abokansa na kusa da nesa.

 *Ya Allah kabamu haqorin rashinsa*

*Ya Allah kai dubun dubata na rahama gareshi*

 *Ya Allah ka haskaka qabarinsa*

 *Ya Allah ka sashi a ceton fiyayyan halita Annabi muhanmad (S)*

 *Ya Allah ka gafarta kuskurensa da namu*

KADUNA PRESS
KNPRSCD 13