Babban sakataren Hizbullah ya bayyana shahadar Sulaimani da Muhandis da cewa ta bude shafin karshen zaman sojojin Amurka  a gabas ta tsakiya.

sakatare Janar din kungiyar gwagwarmayar musulunci ta Hizbullah dake kasar Labanon Sayyid Hassan Nasrullah da yake bayani a wajen zaman makoki na shahadar Janar Qasim Sulemani babban kwamandan dakarun Quds da mukaddashin kwamandan dakarun Hashdu sha’abi na kasar Iraki, ya fadi cewa: wadanan mutane guda biyu sun dade suna burin Shahada musamman a shekarun baya bayan nan , to ga shi kuma hakarsu ta kai ga ruwa, don haka shahadarsu ta bude sabon shifin tarihi ne ga kasashen yankin baki daya.

Har ila yau ya kara da cewa kashe Qasim Sulaimani ta’addancin ne babba a fili, wanda shugaban Amurka Donald Trump ya bada umarni domin kara dagula al’amura a yankin, da kuma rufe kashin da ya sha a yake -yaken da ya kaddamar a kan wasu kasashen yankin, da kuma neman abin da zai fake da shi ganin lokacin zaben shugaban kasa na kara kusantuwa a Amurka.

Ya kuma kara da cewa; Daga lokacin kama mulkin Donald Trump zuwa yanzu ya yi ta ynkurin ganin bayan tsarin musulunci na kasar Iran, amma har yanzu ya kasa cimma burinsa ko da guda daya, takunkumin da kewaye kasar da yayi ba su yi amfani ba, don haka ba shi da abin zai fadawa Amurkawa su yarda da shi.

Har ila yau ya ce Isra’ila  ta dauki Qasim Sulaimani a matsayin babban hatsari amma ta rasa yadda za ta yi da shi wannan ya sa ta nemi mafaka wajen Amurka wajen ganin ta kashe shi, don haka idan sojojin Amurka ba su fice daga Iraki ta hanyar bukatar majalisar dokokin kasar ba, to kungiyoyin gwagwarmaya ba za su taba amincewa wani sojan Amurka guda daya ya ci gaba da zama a Iraki ba.

Daga karshe ya jaddada cewa daukar fansa na adalci shi ne kawo karshen kasancewar sojojin Amurka a yankin baki daya, domin ba za mu dauki fansa akan Amurkawa fararen hula ba, zamu dauka ne kawai akan sojojin Amurka da suka tafka wannan mummunan aikin.