Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

Shugaban Hukumar Leken Asiri Ta Sudan Ya Yi Murabus


Shugaban hukumar leken asiri ta Sudan, ya gabatar da takardar murabus dinsa bayan mutuwar mutane biyar a dirar mikiyan da dakarun gwamntin kasar suka kai kan wasu ofisoshin jami’an tsaron kasar biyu a ranar Talatan da ta gabata.

Janar Abou-Bakr Moustapha, ya mika takardar murabus dinsa ne a jiya Laraba, bayan bata kashin da akayi a cikin ofisoshin guda biyu dake Khartoum wadanda kuma suka kunshi tsohuwar hukumar leken asiri da kuma ta tsaron kasar (NISS).

Da yake tabbatar da hakan, Shugaban majalisar rikon kwaryar kasar, Abdel-Fattah al-Burhan, ya ce su suka bukaci Janar Moustapha ya mika masu takardar murabus dinsa a rubuce, kuma ya aiwatar da hakan.

Ana zargin Hukumar ta NISS, da taka mahimmiyar rawa wajen murkushe masu zanga- zangar da ta samo asali daga karin farashin biredi a a kasar a cikin watan Disamban shekara 2018, wacce kuma ta kai ga tilasta wa sojojin kasar kifar da gwamnatin shugaba Umar Al-Bachir bisa matsin lambar masu boren a watan Afrilun shekarar da ta gabata.

Post a Comment

0 Comments

Close Menu