A yau Alhamis ne dai shugaban kasar Masar Abdulfattah al-sisi ya gana da Firai Ministan kasar Italiya Giuseppe Conte a birnin alkahira inda su ka tattauna rikicin kasar Libya.

Ganawar bangarorin biyu a kasar Masar yana a mastayin yunkurin diplomasiyya da ake yi domin kawo karshen rikicin kasar Libya.

Bangarorin da su ke rikici da juna a Libya su ne janar Halifa Haftar a gabashin kasar,sai kuma gwamnatin Fayez Sarraj da ke birnin Tripoli, kuma take samun goyon bayan Majalisar Dinkin Duniya.

A ranar 13 ga watan Janairu aka yi taron da ya hada dukkanin bangarorin da ke fada da juna na Libya a birnin Moscow na Rasha. Manufar taron na kasar Rasha shi ne tsagaita wutar yaki a Libya, sai dai Janar Halifa Haftar ya ki rattaba hannu akan yarjejeniyar.