Sojojin HKI sun yi dirar mikiya kan Palasdinawa masu zanga-zangar kin amincewa da yerjejeniyar karni a yankin yamma da kogin Jordan. 

Yerjejeniyar wacce Shugaban Amurka Donal Trump ya gabatar da shi a gaban firai ministan HKI benyamin Natanyahu a ranar talatan da ta gabata, ta amincewa HKI kara kwace wasu Karin yankunan Palasdinawa, sannan ta yi watsi da bukatar dawowan dukkan palasdiawa da aka kora daga gidajensu.

A wani labarin kuma kasashen Algeria da Tunisia duk sun yi watsi da yerjejeniyar karni sun kuma nuna goyon bayansu ga al-ummar Palasdinu.