Rahotanni daga kasar ta Yemen sun ce, sojojin kasar ta Yemen sun harbor jirgi maras matukin na Saudiyya ne a yankin Jizan da ke yammacin kasar.

Sa’o’i kadan a baya, dakarun sa kai na “Ansarullah’ a kasar ta Yemen sun harbo wani jirgin maras matuki na Saudiyya a yankin Sa’adah.

Kakakin sojan kasar Yemen Yahya Sari’i, ne ya tabbatar da harbo jirgin sama maras matuki wanda kuma ya bayyana shi a matsayin na leken asiri.

Yahya Sari’i, ya kuma tabbatar da cewa an yi amfani da makami mai linzami ne wajen kakkabo jiragen leken asirin na Saudiyya.

Har ila yau ya kara da cewa a cikin shekarar 2019 da ta shude kadai sojoji da dakarun sa kai na kasar Yemen sun kakkabo jiragen sama marasa matuki har guda 69. Sari’i, ya kuma ce; 53 daga cikin jiragen da aka kakkabo na leken asiri ne sai kuma 9 na daukar hotuna, da kuma 7 masu kai hari.