*TARIHIN SAYYID IBRAHEEM YAQOUB AL-ZAK-ZAKY (H) DA HARKAR MUSULUNCI TANA NIGERIA 🇳🇬*

 *Kashi na biyu 0⃣2⃣*
         
_~Daga Muhmmad Suleiman Abdullah_

~_Bisimillahir Rahamanir Raheem_

*RANA DA WAJEN DA AKA HAIFI SAYYEED ZAKZAKY (H)*

             *HAIHUWARSA.*

An haifi Sayyeed Ibraheem Zakzaky gab da fitowar al'fijir, a ranar talata 15 ga watan sha'aban 1372 hijiriyya, wanda ya yi dai dai da 5 ga watan mayu Shekara ta 1953 miladiyya. An haife shine a unguwar kwarbai da ke cikin garin Zaria jahar kaduna a tarayyar Nigeria 🇳🇬

 *SUNANSA DA LAKUBBANSA.*

Sunan sa Sayyeed Ibraheem Yaaqoub. Yana da laqubba amma wanda ya fi shahara dashi shine Al-Zakzaky: maanarsa mutumin zazzau ko wanda asalinsa daga zaria ne, kuma wannan laqabin na sa na Zakzaky ya samo asali ne tun yana makaranta, wato ya kasance a cikin ajinsu akwai wani dalibi sunansu daya wato Ibrahim Yaaqoub, saboda haka sai aka nemi da su sa wani laqabi wanda zai banbanta tsakaninsu, to shine Malam yasa wannan laqabi na Zakzaky. Bayan haka kuma akwai laqubba da shehu Usman dan Fodiyo  (RA) ya ambace shi dasa a  cikin wasu daga cikin littafansa, wadannan laqabba sune : Sharfudeenee da kuma Ibraheemul magribiy

             *NASABARSA*

Nasabarsa ta wajen mahaifin Sayeed Zakzaky shine dan Malam Yaaqoub shi dan Malam aliy dan Malam Muhammad Tajuddin dan liman Hussaini. Shi liman Hussaini wani bawan Allah ne kuma baban malami da yake limanci a wani masallaci a lokacin. Malam Muhanmad Tajuddin yazo birnin Zaria ne daga Sokoto a cikin tawagar Amir na Zaria. Wato lokacin da Sheikh Usman dan Fodiyo (RA) ya na da mallam Musa a matsayin Amir na lardin zazzau sai ya hada shi da Malam Muhanmad Tajuddin a matsayin mai bashi shawara, da kuma taimaka masa wajen tafi da harkokin jama'a akan tsari na musulunci.

Nasabarsa ta wajen mahaifiya: Sunan mahaifiyar sa malama salaha 'yar Malam Muhanmad Gidado shi kuma dan malam abdul-kadir, asalinsa shima daga Mali yazo Kuma bafulatani ne. Mahaifiyar su Sayyeed Zakzaky sunan ma da aka fi sanin ta dashi  shine (HARI) wannan kalma ce ta fulatanci ma'ana wadda aka Haifa cikin damina. Saboda haka Sayyeed Zakzaky ta wajen uwa da uba bafullatani ne. Mahaifiyar Sayyeed Zakzaky wato malama salaha ta rasu ne a watan November Shekarar 2014.


Mahaifin Sayeed Ibraheem Zakzaky wato Malam Yaaqoub ana kuma ce masa magaji, ya rasu ne tun a watan fabrairu Shekara ta 1972, ya kuma haifi 'ya'ya 16, takwas maza, takwas mata, Sayyeed Zakzaky shine dansa na biyar.

           *TASOWARSA*

Malam ya taso ne, ya kuma girma a cikin birnin Zaria. Tun yana dan yaronsa, an San shi da kyawawa halaye abin yabo, Kuma ya taso Mai kyakkyawan hulda da mutane. Ya kasance yana yawan kai wa 'yan uwansa da kuma abokansa ziyara tun yana yaro Malam (H) ya taso a cikin birnin Zaria a matsayin saurayi Mai aikata duk abinda ya karanta ko yaji daga wajen Malamansa na koyarwar musulunci kuma ya kasance tun yana matashi yana aiwatar da wasu shirye-shirye na musulunci kamar maulidin Manzon Allah da makamantaneu.

A takaice dai kusan rayuwar Malam (H) baki daya a wannan kasa to a Zaria ta kasance, wato in cire wasu ahekaru da yayi su a kurkuku na sashen kasan nan.

Kubiyo mu a rubutu na gaba domin cigaba da wannan rubutun mai Al-barka

 _~Free Sayeed Zakzaky Dolee_

 ~_Daga Muhmmad Suleiman Abdullah_

 _-Kaduna press_

 _KNPRSCD 1⃣3⃣_