Shugaban kasar Amurka Donal Trump yana da shirin kara mutanen daga wasu kasashen duniya, wadanda zai takaita zuwansu kasar Amurka daga ciki har da ‘yan Najeriya.

Jaridar Daily Post ta Najeriya ta bayyana cewa a ranar litinin mai zuwa ce, wato 27 ga watan Jeneru ake saran gwamnatin Amurka za ta bayyana sunayen wasu kasashe 7 wadanda za’a kara kan kasashe 7 na farko wadanda aka hana yan kasashensu zuwa Amurka saboda dalilan tsaro.

A ranar 27 ga watan Jenru na shekara ta 2017 ne shugaban ya takaita zuwan yan kasashe 7 Amurka, jim kadan bayan ya karbi shugabancin kasar. Kasashen dai sun hada da Iran, Libya, Somalia, Siriya, Yemen, Venezuela da Korea ta Arewa.

Amma a hirar da ta hada shi da mujallar “Wall Street Journal” a taron tattalin arziki da ke gudana a halin yanzu a birnin Davos na kasar Switzland,Trump ya tabbatar da cewa zai kara wasu kasashen 7 cikin shirin.

Daily Post ta Najeriya ta ce Sabon hanin zai shafi kasashen Belerus, Myanmar ko Bama, Eriteria, Nigeriya, Sudan, Kirkizistan da kuma Tanzania.

Kafin haka dai kakakin fadar White House, Hogon Gidley ta bayyana cewa matakin ya taimaka wajen kare kasar Amurka sannan ya inganta tsaron kasar