Hukumar UNICEF ta majalisar dinkin duniya mai kula da yara ta bada sanarwan cewa kimanin yara miliyon 2 ne ta yi hasashen zasu rasa rayukansu a tarayyar Najeriya saboda cutar sanyi ko Pneuminia a cikin shekaru 10 masu zuwa.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya NAN ya nakalto hukumar tana fadar haka a jiya Laraba a birnin Kebbi na arewa maso yammacin kasar.

Malam Rabiu Musa, jami’in watsa labarai na hukumar ta UNICEF a Nigeriya ya bayyana cewa rashin samun abincin da ya dace, gurbatan iska da kuma rashin yin alluran riga kafi, na daga cikin abubuwan da za su jawo rasa rayukan wadannan yara idan har ba’a dauki matakan da suka dace tun yanzu ba.

Musa ya ce cutar pneumonia ko sanyi tana da magani, amma kashi 40% na yara kasa da shekaru 5 a kasar ba sa samun alluran raga kafin da ake yiwa yara a irin wadannan shekaru.