Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

An Fara Gudanar Da Gasar Kur'ani Ta Kasa A Yemen

Bangaren kasa da kasa, an fara gudanar da gasar kur'ani ta kasa a Yemen tare da halartar makaranta da mahardata daga sassa na kasar a san'a.

tun a ranar Alhamis da ta gabata ce aka an fara gudanar da gasar kur'ani ta kasa a Yemen tare da halartar makaranta da mahardata daga sassa na kasar a san'a fadar mulkin kasar ta Yemen.

Bayanin yace ana gudanar da gasar ne a bangarori daban-daban, da suka hada da hardar kur'ani mai tsarki a matakai na farko da na biyu da kuma na uku da na hudu.

Haka nan a bangaren karatun kur'ani wato tilawa, ana gudanar da gasar a matakai daban-daban, kamar yadda kuma akwai nauoin tilawa da ake la'akari da su daga masu karatu.

Ana gudanar da wannan gasar ne duk da irin matsalolin da kasar ta Yemen take ciki, sakamakon yakin da kasar Saudiyya take kaddamarwa  akan al'ummar kasar, tare da taimakon Amurka da wasu daga cikin kasashen turawa.

Post a Comment

0 Comments

Close Menu