Bangaren kasa da kasa, an kafa babban hoton Abu Mahdi Almuhandis a filin sauka da tashin jirage na birnin Bagadaza.

An kafa wani babban hoto na Abu Mahdi Almuhandis a filin sauka da tashin jirage na birnin Bagadaza Iraki wurin da Amurka ta kashe shi, wanda hakan ya zo daidai da cikar kwanaki arba'in ne da shahadarsa.

A ranar 3 ga watan Janairu ne Amurka ta kai wa Abu Mahdi Almuhandis tare da Janar Kasim Sulaimani hari a lokacin da suke fitowa daga cikin filin sauka da tashin jiragen sama na birnin Bagadaza, inda a nan take suka yi shahada.