A yau 27/2/2020, ne a kayi jana'izar Shaheed Jawwad Aminu leeman, da misalin karfe goma 10:00am, na safiyar yau alhamis.
Shaheed jawwad yayi shahada ne da yan macin jiya 26/2/2020, sakamakon harin ta'addancin da jami'an yan sanda, tare hadin gwiwan yan kato da gora, da yan iskan gari, suka kawo wa masu muzaharar lumana, na asaki jagoran harkar musulunci a najeriya sheikh Ibrahim zakzaky tare da iyalin sa, anan daura da baking ruwa, da ke kan titin Nmandi Azikwe bypass a nan garin Kaduna.
An yimasa Sallah ne a nan kofar gidan iyayen sa, dake ugwan badiko nan cikin garin Kaduna, Dr Sunusi Abdulkadir kano ne ya jagoraci yimasa sallah, yayin da a ka wuce da shi darurrahma dake ungwan danbo anan cikin grain Zaria, malam Abdulhamid Bello ne ya tarbi gwar sa tare da daruruwa yan uwa daga sassa daban daban a fadin kasar nan.
Muna fatan Allah ya amshi shahadar sa, ya bamu hakurin rashin sa, yasa muyi kyakkyawan karshe irin tasa.
Ya kuma bimana hakkin jinin sa a kan duk Wanda ke da hannu wajen afkar da wannan waki'a.
Allah ka kawa Sayyid Zakzaky lafiya. Ya kuma kubuto mana da shi daga hannun azzalumai.