Antonio Guterres babban sakataen majalisar dinkin duniya ya yi ishara da wata ayar kur'ani a yayin wani jawabinsa.

Babban sakataren majalisar dikin duniya Antonio Guterres ya gabatar da jawabi a gaban karawa juna sani kan sha’anin ‘yan gudun hijira a kasar Pakistan.

A cikin jawabin nasa ya karanto ayar kur’ani mai tsarki, aya ta shida a cikin surat Tauba, da ke cewa; Idan wani daga cikin mushrikai ya nemi mafaka a wurinka to ka ba shi mafaka, domin ya saurari zancen Allah, sannan ka kai shi wuri mafi aminci a gare shi, domin su mutane ne wadanda ba su sani ba.

A cikin bayanin ayar, Guterres ya bayyana cewa, wanann aya tana magana ne kan mutuntawa da kuma girma ‘yan gudun hijira da karbarsu hannu biyu-biyu, maimakon tozarta su da cin zarafinsu.

Ya ce an sanya wannan aya a cikin taken hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta majalisar dinin duniya a 1951, alhali wannan ayar ta sauka ne fiye da shekaru dubu daya da dari hudu da suka gabata.

Babban sakataren na majalisar dinkin duniya ya ce a halin yanzu akwai ‘yan gudun hijira na kasar Afghanistan da dama a Pakistan da wasu kasashe, wadanda sun cancanci kulawa, kuma ya kamata kasasru ta samu aminci da zaman lafiya domin su rayu kamar sauran al’ummomin duniya.

Bisa kididdigar majalisar dinkin duniya ‘yan gudun hijirar Afghanistan miliyan 1.7 a Pakistan, a Iran kuwa akwai kimanin miliyan daya.

Ana gudanar da taro kan ‘yan gudun hijira a birnin Isma abad na Pakistan ne tare da halartar kasashe kimanin 30 na duniya.