A yau Talata 25 ga watan 2 Shekarar 2020, kamar yadda a ka saba daruruwa yan'uwa Almajiran Sheikh Zakzaky, sun fitowa domin cigaba da yin kira ga gwamnatin  kama karyaq da ta gaggauta sakin jagoran harkar musulunci a najeriya Sheikh Ibraheem Zakzaky da mai dakinsa, wanda da take cigaba da tsarewa ba tare da laifin komai ba, tsawon shekaru fiye da hudu.
Sheikh Zakzaky na tsare tun bayan harin ta'addancin sojojin Najeriya karkashin gwamnatin Buhari ta yi a ranar 12/12/2015, da kaisan mabiyan sa sama da dubu, ciki har da ‘ya‘yansa uku, da kona yayar sa da ranta a gaban sa.
A shekarar 2016 babban Kotun dake Abuja ta wanke shi, tace: baiyi laifin komai ba, asake shi. Gwamnatin taki tayi kunnen uwar shegu da maganar.
Bayan duk wannan ta'addancin da gwamnatin buhari tayi, a sun ta kokarin sai sun kashe shi ta hanyar ciyar da shi da shayar da guba. Ga Kuma ma tsanancin rashin lafiyar da yake fama da ita, da iyalin sa. A haka su dauko daga inda suke tsare da shi a Abuja suka dawo da shi kaduna karkashin Nasiru El rufa'i, su ka fa haramtaciyar kotu wai suna tuhumar sa da ingiza mabiyan sa da kisan kai, yayin da a ka ja lokacin a na gudanar da wannan haramtaciyar shari'a da nufin gubar da suka ciyar da shi ya yi tasiri a jikin sa.
Bayan daukar dogo lokaci a gudanar da wannan haramcacciyar  shari'a, kotu ta ba da umarnin a fita da shi waje domin kulawa da lafiyarsa, yayin da gwamnatin ta yi kutsen a can kasar Indiya tare da kawayenta na kasar waje, don ganin sun cike burinsu na ganin bayan sa. Hakan bai yu ba sai suka yan ke shawara dawo da shi gida Najeriya. Suka cigaba da tsare shi ba bisa ka'ida ba.
Da cigaba da haramcaciyar shari'a, Alhamdulillah a wannan makon da ya gabata kotu ta wanke almajiran sheikh Zakzaky, tace basuyi laifin komai ba, anzalunce su, na tsare da akayi tsawon shekaru hudu da watanni. 
Dan haka muke kara kira ga azzalumar gwamnatin kama karya da ta sau jagoran harkar musulumci sheikh Ibrahim Zakzaky da mai dakin sa, domin wannan shari'a ya kara nunawa duniya girmar zaluncin da a kayiwa sheikh Zakzaky da Almajiran sa....
Sannan haka yana nuni da sheikh Zakzaky da mai dakin sa basuyi laifin komai ba.

Yanzu haka dai Sheikh Zakzaky (H) yana gidan kurku a nan garin Kaduna, tare da iyalansa, duniya na ta Kira da a sake shi, amma wannan gwamnatin tana nuna halin ko in kula.

Muzaharar dai ta daga ne da misalin 3:00pm a nan kano road yayin da tayi tafiya mai tsawo har yanbtumatur a nan garin kaduna, sannan akayi jawabi ga al'umar da ke kallo a gefe, sai akayi addu'ah a ka watse

Muna rokon Allah ya kara kunyata makiyan Sayyid Zakzaky.

25/2/2020
KNPRSCD 07
KadunaPress