An daga muzaharar ne a nan gwamna road da ke kan titin Nmandi azikwe by pass a nan cikin garin kaduna, cikin tsari ana tafe ana rera wake a sake shi, ana kuma raba takardu (article) ga jama'ar da ke kallo a gefe.
Zuwan mu masallacin shehu dahiru bauchi ke da wuya, anyi addu'a za a watse sai ruwan harsashi, ta ko ina tare da jifa da duwasu daga yan kato da gora, hade da yan iskan gari, Inda nan take suka shahadan tar Muhammad jawwad Aminu leeman, da raunata yan uwa da dama, sannan sun kama sisters da brothers, har yanzu dai ba musan adadin mutun nawa suka kama ba.
0 Comments