Masu daga nauyi na Iran biyu sun sami kyautukan azurfa biyu a ajin nauyi na kilogram 102 a wasannin shekarar 2020 da ake yi a birnin Tashkent na kasar Uzbekistan.

Mai daga nauyi Hassan Emadi ya gajiya wajen daga nauyi kilo 137 a tashin farko, sai dai a karo na biyu ya sami nasara. 

Bugu da kari ya daga wani nauyin da ya kai kilo 146, sai kuma a karo na gaba da ya kai ga samun kyautar azurfa.

Wani mai daga nau’in na Iran da ya sami kyuatar azurfar shi ne Abulfazl Khakpour, wanda ya daga nauyin kilo 145, 151 da kuma 154.